IYALAN MANZO (S.A.W.W.)

Shafin Farko | ENGLISH PAGE | Shafukan malamai | Littafin maziyarta | Hotuna | Tuntuba | Siyasar Muslunchi | Shahidan Karbala | Photoalbum

Imam Hassan (a.s.), Imam Ali (a.s.) da Imam Hussein (a.s.)

    Allahumma swalli ala Muhammad wa aliy Muhammad.

 Babban makasudin gina wannan shafi shine domin sada al'ummar musulmi da shafukan manyan malamai na musulunci a sassa daban-daban na kasashen duniya. Da kuma bada damar zuwa shafukan musulunci na kungiyoyi da makarantu ko cibiyoyin musulunci na sassa daban-daban.

Muna gabatar maku da sabon shafi na addu'o'i musamman wadanda aka ruwaito daga ingantattun Hadisan Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a.) sai a duba shafin www.addua.org

    Cikin sauki, don yin wannan zagaye na shiga shafukan sai a shiga ta can sama wajan shafin malaman musulunci. Mun gode

Editan shafi  

08088566056


SAKAMAKON JUYAYI DA TAUSAYAWA IYALAN MANZO (S.A.W.W)
                
Manzon Allah (s.a.w.w.) ya fadawa Sayyidah Fatimah (a.s) cewa; a ranar tashin kiyama, zaki shiga tsakanin mata, ni kuma zan shiga tsakanin maza; duk wanda ya zubar da hawayensa don juyayin abin da ya samu Hussain (a.s) zamu kama hannunsa mu kaishi aljanna.    ;-bihar-al-anwar juz’i na 44 shafi na 292.
 
                Ga wandabasu da damar ziyartan kabarin Imam Hussein (as) a ranar Ashura, Imam Baqir (as) ya fadi yanda ya kamata su i ziyararsu kamar haka;
                Mutum zai yi juyayin kashe Imam Hussein (as), ya zubar da hawaye dominsa, ya shirya zaman makoki ta hanyar shirya juyayi da bayyanar da bakin ciki, mutune su sadu da juna a gidajensu, suyi ta’aziyya da juyayi ga juna akan musibar da ta samu Imam Hussein da Iyalansa da Sahabbansa (as).           
                ;-kaamil al-ziyarat, shafi na 175
 
                Manzon Allah (s.a.w.w.) yace “ya fatimah! Kowane idaniya sai ya zubar da hawaye ranar tashin kiyama sai dai kawai idon da ya zubar da hawaye akan abin da ya samu Hussein (a.s), wannan idon zai yi farin ciki.
                      ;-bihar al-anwar juz’i na 44 shafi na 293
 
                Imam li Zainul Abidin (as) yana fada cewa; Duk muminin da ya zubar da hawayensa game da kashe Husseini dan Ali (as) da sahabbansa, ta yanda har hawaye suka zubo a kirjinsa, Allah zai masa masauki a cikin kyawawan dakunan aljanna.
                Imam Muhammad Baqir (as) yace wanda ya tuna mu, ko aka tuna mu a gabansa kuma (sakamakon hakan) har hawaye suka zubo masa daga idanunsa, koda daidai mikidarin fiffiken sauro ne, Allah zai gina masa gida a cikin aljanna. Kuma ya sanya wannan hawaye su zama katanga a wajansa tsakaninsa da wuta. 
                ;- Al-Ghadeer, juz’i na 2 shafi na 202
 
                Imam Jafar Sadiq (as) yace, wanda a gabansa aka ambace mu (da masifar da ta same su) sakamakon haka har idanunsa suka zubar da hawaye, Allah zai haramta fuskarsa daga wuta
                                                                ;-Bihar al-anwar juz’i na 44 shafi na 285
 
                Imam Sadiq (as) yace; Babu wanda zai waka akan Husseini (as) ya yi kuka kuma yasa wasu kuka da ita face sai Allah ya wajabta masa aljanna kuma ya yafe masa zunubansa.
                                                                ;-Bihar-al-anwar.
 
                Imam Ali Reza (as) yace; Duk wanda ranar Ashura ta zame masa ranar bakin ciki, juyayi da kuka, Allah Mai Girma da Daukakazai sanya ranar tashin kiyama ta zamar masa ranar jin dadi da farin ciki.                         
;-Bihar-al-anwar juz’i na 44 shafi na284.
 
                Imam Ali Reza (as) ya fadi cewar da zaran watan muharram ya kama babansa (Imam musa AlKazeem (as))baya kara yin dariya; sai dai juyayi da bakin ciki har zuwa karshen goman farko na watan. Yana kuka da juyayi sosai a ranar goma ga watan. ;-Amaali Saduq shafi na 111.
 
                Imam Reza (as) ya fada wa wani sahabinsa cewa; Idan kana kwadayin ka samu irin sakamakon da yake dai dai da shahidan da aka kashe tare da Husseini (as) to duk lokacin da ka tunashi (Hussein) sai kace “kaico! Ina dama na kasance tare da ku! Da na rabauta da babban rabo”.
                Imam Ali Reza (as) yace masu kuka suyi kuka dominn Husseini (as) domin tabbas, kuka dominsa yana tafiyar da zunuban mutum.                ;-Bihar al-anwar, juz’i na 44 shafi na 284.
 
                Imam Reza (as) yace wanda ya kame daga neman (duniya watau sana, aiki, ko neman) bukata a ranar Ashura, Allah zai biya masa bukatunsa na duniya da lahira.
                                                                ;- wasa’il al shi’ah juz’i na 14 shafi na 504
  
                 
 




SIRRIN AMSAR ADDU’O’I

          Yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci ga shugaban manzanni Muhammad dan Abdullahi baban Sayyidah Fatimah Azzahra (a.s.)

            Allah wanda ya halicce mu ya hori bayinsa da su kira shi akan bukatunsu a kowane hali suke, wadata ko talauchi, tsanani ko dadi. Domin zasu iya gushewa a koyaushe kuma Allah shine zai iya canza wa bayinsa daga dadi zuwa wuya ko wadata da talauchi. Don haka kiranSa madaukaki a kowane lokaci yana da muhimmanci. Haka kuma bawa yana da bukatar fuskantar mahaliccinsa a kodayaushe don neman kariya daga sharrin shaidan da makiya da neman gafarar zunuban da aka aikata. Ana samun yardan Allah ta hanyar kusantarSa. Addu’a tana daga cikin hanyoyi mafi daukaka da girma wajan kusantar Allah.

            Akwai lokuta, wurare, ranaku, addu’o’in da za’a kira Allah dasu don samun ijaba cikin gaugawa kamar yanda Manzo (s) ya yi umarni tare da Iyalan Gidansa tsarkaka (a.s.) kamar yanda zamu kawo a takaice, don karfafawa da buda kofar nazari ga ‘yan uwanmu almajirai.

 

                                    LOKUTAN ADDU’O’I

(1) RANAR JUMA’A

             An samo daga Imam Jafar Sadiq (a.s) yana cewa a tsawon daren juma’a Allah yana kira yana cewa *ko akwai wani bawa na mai imani da zai kirani har zuwa kafin asuba in amsa mas bukatarsa na duniya da lahira, *ko akwai wani bawana mai imani da zai tuba akan zunubansa har zuwa kafin asuba in gafarta masa, *haka Allah zai yi ta kira game da mai bidar arziki, neman lafiya, neman kubuta daga kamu da kuma wanda aka zalunta.

            Imam Baqir (as)ya fada cewa “bawan Allah miminai yana rokon Allah sai Allah Ya yi jinkiri har zuwa Juma’a”.

            Manzon Allah (s.a.w.w.) yana cewa; tabbas juma’a itace shugaban ranaku kuma rana mafi daraja a wajan Allah duk da kuwa tana kasa da idin karama da babbar sallah. Juma’a tana da albarku guda biyar;

            *Allah ya halicci Adam (as) a wannan rana,

            *Allah ya saukar da Adam doron kasa daga aljanna a wannan     

             Rana

            *Allah ya dauki rayuwar Adamu a wannan rana,

            *Akwai wasu sa’o’i a ranar juma’a duk wanda ya roki wani   

             abu

              Wajan Allah zai same shi matukar halas ne,

            *Mala’iku, duniyoyi, kasa, iska, duwatsu da itatuwa suna

             tsoron

              cewa ranar tashin kiyama ta kasance a wannan rana.

 

‘Ya’yan Annabi Ya’aqub (as) sun roki babansu da ya rokar masu gafarar Allah, sai yace”zan rokar maku gafara daga ubangijina” game da wannan sai Imam As Sadiq (a.s) ya ke cewa Ya’aqub (a.s) yayi jinkirin neman gafarar har karshen daren juma’a.

            Akwai wasu sa’o’i a ranar juma’a da ake amsar addu’a da gaugawa, na farko shine a lokacin da liman ya gama huduba ana niyyar kabbara sallar juma’a, na biyun kuwa shine lokacin da rabin jikin rana ya shige giza-gizai yana gab da bacewa daga sama, watau sa’ar karshe ta ranar juma’a.  

 

(2) LOKACIN SALLAR TAHAJJOUD

 An samo hadisi daga manzon Allah (s.a.w.w) yana cewa duk wanda ke da bukata a cikinku, sai ya roka a lokacin sallar dare, domin kune aka baiwa wannan (daukaka) ba a baiwa wadanda suka gabace ku ba.

 

(3) KASHI DAYA NA KARSHEN SA’AR DARE

Manzo Allah (s.a.w.w) yace “a kowace sa’ar karshen dare Allah yana kira ko akwai wanda zai kirani in amsa masa, ko akwai wanda zai roke ni in bashi, ko akwai wanda zai nemi gafarata in gafarta masa, ko akwai wanda zai tuba in amshi tubarsa?”

Imam Sadiq (a.s) yana cewa “ kar kubar idanunku su shagaltu da barci, domin idanu su masu karancin godiya ne ga Allah” Manzon Allah (s..a.w.w) yana cewa “lokacin da mai imani na gaskiya ya tashi don kusantar Allah da nafilar dare a bayan tsakiyar dare alhalin barci na cin idanunsa, Allah zai yi magana cikin alfahari ga mala’ikunsa cewa ‘kunga bawan can nawa wanda ya tashi don yin sallar da ba farilla ba? Don haka na sanya ku zama shaida na gafarta masa zunubansa.’”

 

(4) RANAKUN IMAMAI (A.S)

            Kowace rana an kasa ta zuwa awa sha biyu, kuma kowa ce an dangantata da wani Imami, watau tana da alaka dashi. Haka ma ranaku suna da alaka da Imamansu don haka yana daga cikin hanyoyin ijaba da gaugawa a roki Allah da tawassuli da Imamin dake da alaka da ranar. Sayyid Ibn Tawous ya fada a cikin Mufatihul Jinan, haka ma a littafin ‘MESBAH’ ga yanda kason ranakun yake

Asabar- Manzon Allah (s.a.w.w)

Lahadi- Imam Ali (a.s)

Litinin-Imam Hassan da Hussain (a.s.w.a)

Talata-Imam Zainul Abdin , Baqir da Jafar as Sadiq (a.s.w.a)

Laraba-Imam Kazim, Reda, Jawad da Hadiy (a.s.w.a)

Alhamis-Imam Hassan Askari (a.s)

Juma’a- Imam Mahdi (a.t.f)

 

(5) DARAREN LAILATUL QADR

            Wadan nan wasu darare ne masu matukar ijaba da amsuwar addu’a da gaugawa kamar yanda yazo a ruwayoyi da dama. Wannan dare zai kasance a daya daga cikin darare uku ne kamar yanda yazo a ruwayar Iyalan gidan Manzo. Daren 19 , 21 ko 23 na watan Ramadan. Don haka aka yi umarni da a raya dukkan kowane daya daga cikin wadannan dare uku. Akwai ma ruwaitattun addu’o’i da aka kwao a littattafan addu’o’i irin su ‘mufatihul jinan’ da ‘mesbahul mutahajjud’

 

(6) DARAREN RAYAWA

            Akwai ma wasu dararen da aka so a raya su da ibadu, zikirori da addu’o’i don darajar dararen a wajan Allah (T). Wadannan darare sune

*daren farko na watan Rajab

*daren Nisfu Sha’aban (15 Sha’aban)

*daren karamar sallah

*daren babbar sallar 

 

(7) RANAR   ARFAH

            Rana ce da ake son a yawaita addu’o’i da ibadu tare da yin azumi a wannna rana, akwai ijaba sosai ga addu’o’in da aka yi a wannan rana.

 

(8) WASU YANAYI NA AMSAR ADDU’O’I

            Akwai samun dacewa na amsuwar addu’o’i a cikin wasu yanayi da suka hada da;

@ lokacin da iska ta kekadawa,

@ lokacin da ruwan sama yake zuba,

@ lokacin da ake kiran sallah da kuma

@ lokacin da jinin shahidi yake zuba.     

            Domin a daidai wannan lokaci kofofin aljanna suna a bude ne kamar yanda aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s)   

(9) ALFIJIR ZUWA FITOWAR RANA

            Abul Sabak Kanani ya ruwaito daga Imam Baqer (a.s)yana cewa Allah yana amsawa bayinsa masu yawaita addu’a, don haka kuyi addu’a da asuba har zuwa fitowar rana, saboda kofofin aljanna suna bude ne wannnan lokaci, ana raba arziki kuma ana biyan bukatu. 

 

(10)    BAYAN SALLOLIN FARILLAH      

Yana da matukar muhimmanci a yawaita addu’a a bayan sallolin farillah, domin hakan yana da muhimmmanci shine ma yasa wasu littattafan suka ruwaito addu’o’in da manzo (s) yake karantawa bayan kowa ce sallah.

 

KARIN BAYANI       

 

  1. Akwai wasu addu’o’i masu dauke da sunan Allah mafi girma da in har aka kira shi dasu zai amsa da gaugawa, daga ciki akwai ;-           

      ‘Ya Hayyu ya Qayyum’, Ya zaljalali wal ikram’, ‘Ya huwa ya man la huwa illa huu’  fadar ‘ya rabb’ sau goma ko ‘ya Allahu’ shima goma.

 

 

  1. Akwai wasu addu’o’i masu matukar ijaba don kasancewarsu saukakku ga manzo da iyalansa ko kuma ma’asurai, kamar irinsu addu’ar kumail, mashlool, sammat, mi’iraj’ azumal bala’ da makamantansu.
  2. Ana son yin addu’a a wasu bagire na musamman domin matsayinsu ga Allah da kuma amsuwar ita addu’ar take yanke domin matsayin wurin kamar irin su filin arfa, masharul haram, masallaci da kuma kusa da kabarin Imam Husaain. Kamar yanda wata rana Imam Sadiq ya bukaci ayi masa hayar wani yaje yayi masa addu’a a kabarin Imam Hussain (a.s) shine mutumin yake mamaki har ya tambayi Imam din shine ya amsa masa da cewa ‘wannnan mutum ya fadi gaskiya, sai dai bai san cewa ba Allah yana da wasu wurare na musamman dayake amsaraddu’o’i, kabarin Imam Hussaini yana daga cikinsu’
  3. Har wala yau yakini shine ginshikin amsuwar addu’a, domin duk wanda yake rokon Allah ya koma yana kokwanton amsuwar to tamkar bai yi imani da lakawarin Allah bane da yace ku rokeni zan amsa maku (Allah ya tsaremu). Masu yakini suna tare da kwanciyar hankali da natsuwa tun bayan da suka gama sanar da Allah bukatunsu.

 

 

  *****Don neman karin bayani da ilimintuwa game da abin da ya shafi addu’o’i da Iyalan Manzo sai a duba wadannann shafuka na yanar gizo (Internet)

1.www.duas.org

2.www.duas.8m.com


Tarihin Ma'asumai Goma Sha Hudu


                          1.       ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.A)

Alkunyarsa----------Abul Kasim

Mahaifinsa-----------Abdullahi

Mahaifiyarsa--------Aminatu ‘yar Wahab

Ranar haihuwarsa-17 Rabiul awwal shekarar giwaye

Ranar wafatinsa---- 28 Safar shekara 11 bayan hijra.

Kabarinsa------------Madinatul munawwara (Saudiyya)

                                                2. SAYYIDAH FATIMA AZZAHRA (A.S)

Alkunyarta---------- Ummu Abiha

Mahaifinta-----------Annabi Muhammad

Mahaifiyarta--------Khadijatul Kubra

Ranar haihuwarta-20 Jimada Sani, shekara 5 bayan wahayi

Ranar shahadarta- 3 Jimada Sani, shekara 11 bayan hijra

Kabarinta-----------makabartan Baki’a (birnin Madina a Saudiyya)

                                                  3. IMAM ALI AMIRUL MUMININ (A.S)

Alkunyarsa---------- Abul Hassan

Mahaifinsa-----------Abu Talib

Mahaifiyarsa-------- Fatima ‘Yar Assad

Ranar haihuwarsa- 13 Rajab, shekara 10 kafin wahayi

Ranar shahadarsa- 21 Ramadan, shekara 41 bayan hijra

Kabarinsa----------- Najaf (Iraki)

                                                4. IMAM HASSAN ALMUJTABA (A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Muhammad

Mahaifinsa----------- Ali bin Abu Talib

Mahaifiyarsa-------- Fatima az- Zahra

Ranar haihuwarsa- 15 Ramadan, shkara 3 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 7 Safar, shekara 50 bayan hijra.

Kabarinsa----------- Madina (Saudiyya)

                                                5. IMAM HUSSAIN ASSHAHID (A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Abdullah

Mahaifinsa----------- Ali bin Abu Talib

Mahaifiyarsa-------- Fatima az-Zahra

Ranar haihuwarsa- 3 Sha’aban shekara 4 bayan hijra

Ranar shahadarsa-  10 Muharram, shekara 61 bayan hijra

Kabarinsa----------- Karbala (Iraki)

                                                6. IMAM ALI ZAINUL ABIDIN (A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Muhammad

Mahaifinsa----------- Hussain bin Ali

Mahaifiyarsa-------- Shahr Banu

Ranar haihuwarsa- 5 Sha’aban, shekara 38 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 25 Muharram, shekara 94 ko 95 bayan hijra

Kabarinsa----------- Madina (Saudiyya)

                                                7. IMAM MUHAMMAD AL-BAKIR

Alkunyarsa---------- Abu Jafar

Mahaifinsa----------- Ali bin Hussain

Mahaifiyarsa-------- Fatima ‘yar Imam Hassan

Ranar haihuwarsa- 1 Rajab, shekara 57 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 7 Zulhijja,  shekara 114 bayan hijra

Kabarinsa-----------  Madina(Saudiyya)

                                                8. IMAM JAFAR AS-SADIK (A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Abdullah

Mahaifinsa----------- Muhammad bin Ali

Mahaifiyarsa-------- Ummu Farwah

Ranar haihuwarsa- 17 Rabiul awwal, shekara 83 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 25 Shawwal, shekara 148 bayan hijra

Kabarinsa----------- Madina (Saudiyya)

                                                9. IMAM MUSA AL-KAZIM (A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Ibrahim

Mahaifinsa----------- Jafar bin Muhammad

Mahaifiyarsa-------- Hamidah

Ranar haihuwarsa- 7 Safar, shekara 128 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 25 Rajab, shekara 183 bayan hijra

Kabarinsa----------- Kazimiya (Iraki)

                                                10. IMAM ALI AL-RIDA

Alkunyarsa---------- Abul Hassan

Mahaifinsa----------- Musa bin Jafar

Mahaifiyarsa-------- Ummul Banin Najmah

Ranar haihuwarsa- 11 Zulkida, shekara 148 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 17 Safar, shekara 203 bayan hijra

Kabarinsa----------- Mash-had (Jamhuriyar Musulunci ta Iran)

                                                11. IMAM MUHAMAD AL-JAWAD (Attaki)(A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Jafar

Mahaifinsa----------- Ali bin Musa

Mahaifiyarsa-------- Sabikah

Ranar haihuwarsa- 10 Rajab, shekara 195 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 29 Zulkida, shekara 220 bayan hijra

Kabarinsa----------- Kazimiyya (Iraki)

                                                12. IMAM ALI AL-HADI (Annnaki) (A.S)

Alkunyarsa---------- Abul Hassan

Mahaifinsa----------- Muhammad bin Ali

Mahaifiyarsa-------- Sumanah

Ranar haihuwarsa- 2 Rajab, shekara 212 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 26 Jumada Sani, shekara 254 bayan hijra

Kabarinsa----------- Samarra (arewaci Bagadaza)(Iraki)

                                                13. IMAM HASSAN AL-ASKARI (A.S)

Alkunyarsa---------- Abu Muhammad

Mahaifinsa----------- Ali bin Muhammad

Mahaifiyarsa-------- Hadisah

Ranar haihuwarsa- 8 Rabiul Sani, shekara 232 bayan hijra

Ranar shahadarsa- 8 Rabiul Sani, shekara 260 bayan hijra

Kabarinsa----------- Samarra (Iraki)

                                                14. IMAM MUHAMMAD AL- MAHDI (A.T.F)

Alkunyarsa---------- Abul Kasim

Mahaifinsa----------- Hassan bin Ali

Mahaifiyarsa-------- Narjis

Ranar haihuwarsa- 15 Sha’aban, shekara 255 bayan hijra

                                                    Har yanzu kuma yana raye.


SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

KO KASAN Shugabanni goma sha biyu da Manzo yayi wasiyyar zasu bayyana bayan wafatinsa ? Wadanan sune Imam Ali (as),Imam Hassan (AS),Imam Husseini Shahidin Karbala (as),Imam ali Zainul Abidin (as),Imam Muhammad Albaqir(as),Imam Ja'afar Assadiq (as),Imam Musa Alkhazim (as),Imam Ali Ridha (as),Imam Muhammad Aljawad (as),Imam Ali Naqi (as),Imam Hassan Askari (as),Imam Muhammad Almuntazir Almahdi (as)