SABUWAR GABAS TA TSAKIYA: INA AKA KWANA?
Tsohuwa jawarar nan ta kasa Amurka, kuma ‘yar amshin shatan Amurka Mr. Bush, wadda kuma ake kira a gabas ta tsakiya da “Hammalatul hadab” ko kuma in yi barobaro nace ina nufin Condelezza Rice, a cikin watan Yuli ne ta bayyana cewa yakin da ake tsakanin Hizbullahi da Isra’ila wani yunkurine na haihuwar wata sabuwar gabas ta tsakiya.
Tun kafin wannan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila (HKI) tayi da baradan nan Hizbullahi akwai wasu alamomi da suka nuna Amurka da kawayenta suna da wani mummunan kuduri ga yankin, sai kuma gashi ta bayyana cewa shirin yana da nasaba da haihuwar sabuwar gabas ta tsakiya ne. Sai dai abin tambaya shine; mi suke nufi da sabuwar gabas ta tsakiya ne? Wannan ya yiwu itace tambayar da mafiya yawan jama’a suka rinka yi bayan jin waccan manufa.
Sabuwar gabas ta tsakiya, ko faffadar gabas ta tsakiya, suna nufin gabas ta tsakiya mai dauke da zallan mulaka’u (masu mulki) ‘yan amshin shatan Amurka, kawar da dukkan malamai masu yunkurin raya addinin musulunci a zukatan al’umma, share duk wata gwagwarmaya ta neman ‘yanci, kawar da duk wasu masu kishin adddinin musulunci a yankin tare da share tasirin addinin musulunci a zukatan al’ummar yankin, share duk wasu alamomin addini ko da kuwa gine-gine ne a yankin, samar da damar tatse arzikin yankin musamman man fetur da Allah Ya albarkaci yankin da shi, sanya wa al’ummar takunkumi a bakunan mutanen yankin musamman ta fuskacin siyasa, ci gaba da addini, samar da biyayya ga sabon musuluncin da Amurka ke shirin haihuwa, kauda dogaro da kai ga mutanen yanki, dawwamar da HKI a yankin ba tare da daga mata ko da yatsa ba daga wata kasa, fadada HKI a yankin ta hanyar mamaye kasashen makwabtanta kamar su Lebanon, Palasdinu, Siriya, Jordan, Iraki dss, samar da ‘yan siyasa kuma ‘yan koren Amurka wadanda a shirye suke su saida mutuncin al’ummarsu kamar dai su Kharzai ( samar da wasu kharzanonin a sauran kasashen musulmi irin su Palasdinu, Lebanon da Iraki, dss).
Wannan yunkuri na haihuwar sabuwar gabas ta tsakiya ya fara fitowa a fili ne tun lokacin da aka shirya hari akan dogayen gine-ginen Amurka da “pentagon” ran 11 ga satumban 2001. Wannan ya haifar da haihuwar Osama bin Laden da kungiyar nan tasa AlQa’ida da C.I.A.(kungiyar leken asirin Amurka) ta haifa a cikin labule. Bayan faruwar al’amarin ne sai Mr. Bush (wanda shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya kira da shaidani) yace zai yi yakin “Crusade” sakamakon wannan harin, idan aka duba “dictionary” ma’anarsa shine yakar addinin musulunci. Kalaman nasa sun yadu a kafafen yada labarai.
Wannan ya haifar da Amurka ta jagoranci munanan kashe kashen rayuka masu yawan gaske , azabtarwa, kame-kame, rushe-rushen gidaje, ruwan bama bamai akan fararen hula da yawansu mata da yara da tsofaffi a kasashen Afganistan da Iraki, a gefe guda kuma ga Israila na cin karenta babu babbaka a kasashen Palasdinu da Lebanon an kuma hana wata kasa tayi mata koda harara.
An dai yi ta ruwan bama- bamai a yankin tun daga bayan satumban 2001 kama daga bama baman “nail bomb”, “chemical bomb”, “cluster bomb”, “uranium bomb” da makamantansu. Amurka tamaida yankin wata cibiyar hada hadar makamai ita da kawayenta, a yayinda HKI ma ta amshi nata tallafin makaman don wancan kuduri daga hannnun Amurka a watan Yuli 2006 a matsayin karin kaso. Haka ma a ranar 25 ga watan yulin jiragen Amurka biyar ne suka tashi daga sansanin sojin Amurka na Saudiyya da Qatar dauke da ton ton na mugayen makamai don kai tallafi ga HKI . Bayan wadan nan ma wasu jiragen dauke da makamai har yada zango sukayi don hutawa daga Amurka akan hanyarsu ta zuwa HKI.
A lokacin da aka sanya wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran karan tsana da barazana kan shirinta na makamashin nukiliyar zaman lafiya ita HKI nada damar kera wadancan mugayen makamai kuma an hana hukumar binciken ta IAEA da ce mata uffan a makerarta dake Dimona kusan sama da shekaru 40.
A duk lokacin da HKI ta kai farmaki kan raunannan al’ummar fararen hulan Palasdinu ko Lebanon sai Amurka da kawayenta suce tana kare kanta, a yayinda sukuma musulmin yankin aka hana masu wannan ‘yanci na kare kai. In kuwa har suka maida martani to sunansu “yan ta’adda” “tsageru” “masu tsattsauran ra’ayi” “masu zazzafan ra’ayi” da makamantansu kuma a shelanta cewa kawar da su ya zama wajibi, kuma dole ne kowa ce kasa ta taimaka a kan haka, ciki kuwa harda NATO da kasashen larabawa. Wannnan dai duk yana da nasaba da yunkurin haihuwar ita waccan sabuwar gabas ta tsakiya ne.
Sai dai Bush da Hammalatul Hadab (condalezza) sun yi aman da suka shelanta wa duniya sunyi shi kuma suka kwashi daagwalonsa suka kai wasu kasashe lokacin da rundunar Hizbullahi suka bayyana kama sojojin HKI 2 da kashe 8 a lokacin da suka shigo yankin kudancin Lebanon don ayyukan ta’addanci kamar yanda suka saba. Kowa ya sani cewa HKI ba tana tura sojojinta makwabtanta bane don samar da zaman lafiya, sai dai faruwar hakan ya basu damar su bayyana wa duniya wannnan mafarki da suke na haihuwar waccan cikin shege da suke kokarin haihuwa. Wani abu shine, an dai gwabza yaki, anyi gumurzu, anyi ruwan bama-bamai da rokoki har na tsawon kwana 34 amma waccan nakuda bata kare ba, ina ma tunanin yanzu sun gano cewa wancan cikin fa ya zube kuma ba za’a taba samun wani ba matukar akwai dakaru tsayayyu irin Hizbullahi da Hamas (da tace sambata yarda da kasantuwar HKI ba) a yankin, ko akwai irinsu AhmadiNejad na Iran ko su Muqtada As Sadr a Iraki. Duk manufofin da aka ce sune dalilin wancan yaki ba a cimma ko da daya ba, Misali maganar kwato sosjojin HKI biyu har aka gama ba a amsosu ba, kamar yanda Sayyid Nasrullah yace duk duniyar nan babu karfin da zai iya kwato su sai dai ta hanyar tattaunawa ta shiga tsakani, kuma har yanzu a haka ake. Haka ma manufar da suka shelanta na gusar da Hizbullahi daga kudancin lebanon ko kuma raba su da makamai, kafin ma a dakatar da wuta yawan makaman da Hizbullahi suka rinka harbawa yafi na farkon fara yakin.
Su kuwa dakarun HKI musamman wadanda akewa kirarin da babu kamarsu a duk yankin “Golani Brigade” sai da suka kawshi hannunsu a hannu ta yanda suka rinka gudu suna barin filin daga, ance don bakin cikin wannnan rashin nasara yasa daga baya wasu ma cikinsu suna kashe kansu. Tankar nan ta Merkava kirar HKI da take da tsada da kwarjini a kasashen duniya ta wulakanta a hannun Hizbullahi ta yanda rokokinsu ke mata dai dai. Wannan ya nuna wancan ciki ya gamu da mummunar nakudar da za a dade ba a daina jin radadinta ba, kuma za a dade ba a kara tunanin samar da irin wancan ciki ba. Yanzu dai ya zube, ya bare kuma ya daidaice warwas. Sai dai tarihi ya tuno da abin da suka faru a lokacin nakudar cikin da Hizbullahi suka yi barinsa.
A wancan lokacin sojojin HKI sun yita jefa takardun gargadi ga al’ummar kudancin Lebanon wai su fice daga gidajensu in kuma sunki to munanan hare-haren da zasu mai a yankin zai shafesu. Tayiwu sun so share yankin ne don samar da sababbin mazaunan yahudawa ‘yan share wuri zauna kamr yanda suke yi a Palasdinu kamar garuruwan kewayen Gaza, Rafah da Al Areesh. Amma wani abin ban sha’awa, mazauna yankunan na kudancin Lebanon suka ce ba inda zasu, ba domin komi ba sai don kudurin cewa ai sojojin Hizbullahi ‘ya’yansu ne duk abinda zai samesu to ya same su tare. Wannan bai yiwa HKI dadi ba shi yasanya ma suka dinga harba mugayen bama-bamai a gidajen da suke tunanin an tara yara, mata da tsofaffi, kamar harin zaluncin da suka kai a garin Qana wanda yayi sanadiyyar shahadar mutum wajan 60 mafiya yawa mata da yara.
Ta daya bangaren kuma, ba zamu manta da gudunmuwar da wasu shugabannin kasashen larabawa suka bada ba a wajan yunkurin nakudar haihuwar wannan cikin shegen Mr. Bush da ya bare. Wannan kuma yana da nasaba da halayyarsu ta munafuntar juna da kuma watsi da adddinin musulunci tare da kokarin kare kujerar sarautarsu ta kowa ce hanya. Mr. Bush yana kiransu ya yi masu jankunne na musamman, kuma yana yi masu kurari da mazurai akan su tullafawa duk shirinsa a yankin gabas ta tsakiya. Ko a watan satumba 2006 lokacin taron majalisar dinkin duniya, shugaban Pakistan Musharraf ya fada wa manema labarai a Amurka cewa Mr. Bush yace masa indan bai taimaka a kan yakin da ake da Afghanistan ba to shima zai kai masa hari. A duk yankin gabas ta tsakiya jamhuriyar Musulunci ta Iran ce kawai sai Siriya kasar Amurka da HKI suke saurara wa shugabanninsu don kuwa shima Mr. Bush ya samu labari tun daga kakanninsa cewa wadan nan kasashe ba zasu taba rankwafawa zaluncin shaidanun duniya ba. Dalilin kuwa baya rasa nasaba da cewa sune ake da tabbacin suna da shugabanni a mafiya yawan kasashen yankin wadanda masu mulkin kaar basu da salsalar jini da yahudawa.
A Kasar Masar, wanda akewa kirari da “sa mai dariyar keta” Hosni Mubarak lokacin wancan fafatawa da dakarun na Hizbullah cewa yai “ Masar ba zata yi fada da Israila ba saboda Hizbullah, na kuma tabbatar da Israila ba zata yaki da Masar ba”. Haka kuma, Masar din ta bada mashigar hanyar ruwan nan na “Suez Canal” don bada dama ga Amurka ta wuce da jiragen makamanta na tallafi ga HKI, an ruwaito cewa a ranar ma, an hana duk wata zirga-zirga a yankin don farantawa a Amurka da HKI.
Saudiyya kuwa, har su “Sheikh” (sahibul shirk wal haram) suka fitar da fatawa bisa umarnin gwamnatin kasar don farantawa iyayen gidansu. Fatawar da Sheikh Abdullah bin Jibrin cewa tayi “haramun ne a goyi bayan Hizbullahi ko a yi masu fatar samun nasara.” Manya kaji masu addini.
Masarautar Jordan kuwa har mitin suka gudanar a asirce da HKI don nuna masu goyon bayansu a wannan yaki. Ga kuma labaran da suka fito cewa gwamnatin Amurka na tafiyar da wasu gidajen yarin asiri a kasar da tallafin masarautar ta Jordan.
Tarayyar Daular Larabawa U.A.E. da Kuwait duk sun bayyana goyo baya ga yunkurin wancan shegen ciki da aka yi bari. Don kuwa ance jiragen makaman Amurka sun rinka tashi daga tarayyar daular larabawan don tafiya Isra’ila.
Yanzu dai wannan yunkuri yaci tura kuma ya bar baya da kura, don kuwa yanzu haka HKI nacan tana jinyar mummunan galabaitar da tayi ta kowace fuska, a Amurka kuwa tasirin Mr. Bush ya fadi kasa warwas kuma harkokin siyasarsa sun kara dagulewa, zaluncin Amurka ya kara fitowa fili, munafunci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kara bayyana. A kasashe irin su Canada, Amurka, Ingila, Jamus da wasu da yawan kasashen turawa an fito ana tir da ‘yan Iskan da ke kokarin tallafawa nakudar cikin shegen su Mr. Bush.
Yanzu dai wancan yunkuri bai yi nasara ba, sai dai abin tambaya shine, shin anya kuwa akwai yuwuwar wadancan kawalai, ‘yan daudu da ‘yan tashan wancan cikin shege sun hakura. “Abin da kamar wuya” wai gurguwa da auren nesa. Sai dai yana da kyau kamar yanda al’ummar duniya ta farka don yin Allah wadai da wancan yunkuri to asake kasancewa kamar haka a nan gaba idan wadacan kawalai sun sake yunkurowa. Don kuwa wannnan wani tsohon shiri ne da yahudawa suka dade suna mafarki na samar da “israila babba”, kuma akwai yiwuwar hannun Amurka da Birtaniya dumu dumu a kokarin cimma wancan mugun kuduri na yahudawan sahayoniya. Yanzu haka ta bayyana akwai makaman da ake aiki dasu don wani sabon yunkurin, don haka yana da kyau a sa ido sosai a garesu da fahimtar duk wata manufa tasu da idon basira, tare da farkar da al’ummar musulmi akan wannan. Makaman yunkurin kuwa sun hada da Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kamar yanda kwamitin ya zama rakumi da akala a hannun Bush da Blair. Osama bin Laden da su Ayman Al-Zawahiri duk akwai yuwar kungiyar leken asirin Amurka na amfani dasu don cimma manufofinta (watau C.I.A.), MOSSAD, tare kuma da Kharzanonin gabas ta tsakiya. Addu’a tana da tasiri ga muminai sosai, don haka a kullum kar mu manta da ‘yan ‘uwanmu Mujahidai a duk inda suke. Allah Ya taimaki Mujahidai.
Ga wasu muhimman bayanai a shafukan yanar gizo;
1. Bayanin Sayyid Nasrullah a ranar taron murnar nasrar Hizbullah
http://www.moqawama.org/english/_amen222.php?filename=20060926170043026
2. Bayanin gargadi da jan kunnen da Dr. Ahmadinejad yayi wa taron
majalisar dinkin duniya game da ta’addancin Amurka da HKI
(a) na film http://www.un.org/webcast/ga/61/gastatement19.shtml
(b) na rubutu http://www.un.org/webcast/ga/61/pdfs/iran-e.pdf
3. Murnar nasarar Hizbullahi a karkashin jagorancin harka islamiyya a nijeriya
http://www.islamicmovement.org/sheikhonhizbullah.htm
http://www.harkarmusulunci.org/labarai19.htm
http://www.harkarmusulunci.org/labarai19.htm
4. Gargadin Sayyid Fadlullah ga Bush da Israila a hudubar juma’a
http://english.bayynat.org.lb/FridaySpeeches/index.htm
5. Imam Khamne’I (KS) ya jinjina wa Hizbullah
http://www.alwilayah.net/qaid/labarai/qaid-zahra06.html