A ranar 9 ga watan Muharram, kwamandojin sojin Yazidu (LA) suka fara kada kugen fara yakar Imam Hussain (AS) dan Fatima az Zahra diyar Manzon Allah (s.a.w.a.). Imam Hussain ya kira dan’uwansa Abbas a daidai wannan lokaci yace masa “ya Abbas! kaje ga kwamandojin sojojin Yazidu, ka tambayesu su yi mana Karin jinkirin dare daya, har zuwa gobe”. Abbas ya tafi zuwa ga wannan bukata ta Imam Hussain. Hakan kuwa ta samu.
Shin Imam Hussain yana neman Karin jinkiri ne domin kara samun damar ganawa da iyalansa? musamman karamar diyarsa Sakinah da bata iya barci sai akan kirjinsa? Amsa dai shine a’a, ko alama ba haka abin yake ba. Ai Imam Hussain yana neman Karin jinkirin lokaci ne domin Karin munajati da ubangijinsa da kuma jiran wani bakonsa na musamman; HUR BIN YAZID.
Hur shine farkon kwamandan sojojin Yazidu wanda ya fara tare Imam Hussain ya hana shi wuce wa zuwa Kufah. Ya tilasta wa Imam Hussain yada zango a Karbala. Ma’anar Hur shine ‘yantacce, ya ‘yantar da kansa daga wuta tun kafin lokaci ya kure. Hur ya koya mana muhimmin darasi a rayuwa. Ya kasance yana fuskantar zabi tsakanin wuta da aljanna, tsakanin gaskiya da bata, tsakanin zalunci da shiriya, tsakanin duniya da lahira, tsakanin shahada da matsayin gidan duniya. Amma sai Hur ya zabi aljanna akan wuta, gaskiya akan bata, shiriya akan zalunci, lahira akan duniya, shahada akan duniya, ya yarje ya tafi wajan Allah yana shahidi madaukaki da rayuwa cikin zilla.
A yau cikin rayuwar da muke muna iya fuskantar ire-iren wadannan kalubale da Hur ya fuskanta, don haka tarihin rayuwar wannan bawon Allah Hur bin Ziyad ya koya mana irin zabin daya kamata muyi.
Ranar 9 ga Muharram ta kasance rana mafi tsanani daga cikin ranaku na bakin ciki musamman kasantuwar ita ce rana ta biyun karshe a duniya ga Imam Hussain da sahabbansa, ita ce ranar da tafi sauran ranakun da suka gabace ta tsanani kan musgunawa da cutarwan da aka yi wa Imam Hussain da Iyalansa da wadanda suke tare da shi. A wannan rana yara kanana sun rinka kuka suna kiran ruwa saboda kishirwan da ke damunsu, suna cewa ‘Al-atash! al-atash!, al-atash!’ Wannan kuka na kananan yara ya rinka isa har kunnuwan sojojin Yazidu da suka hana su koda makwalwa daya na ruwa daga kogin Furat.
Wannan sauti mai tada hankali ya rinka isa har kunnuwan Hur, wanda a daidai wannan rana yana cikin sojojin Yazidu, hakan yasa hankalinsa ya rinka tashi, yana tunani cikin zuciyarsa, yana Magana da ita kan kuskuren day a aikata. Hur yana cewa “mi ya ja mani? Mi yasa? Mi yasa na sanya dan Fatima a wannan matsayi? Shin Hussain zai yafe mani? Allah zai yafe mani? Yaya zan yi na nemi gafara?” A haka dai Hur ya share wannan dare yana ta tunani, yana kuka da neman gafarar Allah akan wannan kuskure da yayi.
Ranar 10 ga Muharram dokunan sojojin Yazidu, tun kafin fara yaki suka fara tsalle, basu iya tsayawa a wuri daya saboda tsananin zafin rana da ke damunsu a kofatonsu. Sojojin Yazidu suka fara debo ruwa daga kogin Furat suna zubawa kafafu da kofaton dokunansu domin su samu saukin zafi.
Hur sai ya fara tsunduma cikin tunani akan abinda yake gani da idanunsa, a lokacin da yake jin kukan Iyalan Manzon Allah saboda kishirwa sai yaga ana zuba ruwa ga dokuna domin suji saukin zafin rana a kafafunsu. Hur yana tunani a ransa “ruwa mai yawa ga dabbobi, alhalin ‘ya’yan Sayyida Fatima suna kuka kan ruwa dan kalilan. Za’a iya baiwa dabbobi ruwa mai yawa, amma jikokin Manzon Allah an hana su”. Wannan zalunci ya kara firgita Hur tare da tada masa hankali.
A haka dai Hur ya kasa jure wa abinda yake ji da gani da idanunsa na zalunci, sai ya yanke shawarar canza zabi, ya kira dansa yace “ya dana, nayi babban kuskure. Na tare wannnan mumini mai tsarki a nan don a kashe shi. Ya dana , Don Allah, ka yi sauri ka kaini wajan Imam Hussain in roki gafara a wajansa tun kafin lokaci ya kure, ina jin kunyar abin da na aikata. Shin Hussain zai yafe mani? Da wace fuskar zan fuskance shi?”
Hur yaci gaba da cewa “ya dana, kafin ka kaini ga Hussaini, ka daure mani hannayena kuma ka rufe mani fuskata, ta yanda ba zanyi ido biyu da shi ba a lokacin da nake neman gafara.”
Wannan da mai biyayya ya aikata duk yanda babansa ya umarce shi. Ya dauko igiya ya daurewa babansa hannaye, ya sa kyalle ya rufe masa fuska kamar yanda ya umarceshi. Ya kama igiyar yana ja ya tafi dashi gaban Imam Hussain.
Abul Fadl Abbas, babban kwamandan Imam Hussain, yana tsaye ya hango mutum biyu na nufo inda suke daga rundunar Yazidu, sai ya fitar da takobinsa daga kubenta yana gargadinsu da su tsaya inda suke. Imam Hussain yana kallon abinda ke faruwa, sai ya taho zuwa ga Abbas yana cewa “Ya dan’uwana Abbas! mai da takobinka, wadannan mutane ba sunzo yakarmu bane. Hur ne bako na na musamman , shi nake jira, muje mu karbesu ya Abbas!” Imam Hussain da Abbas suka kama hanya domin tarban wadannan baki nashi. Suna isa Imam Hussain yace “sannu da zuwa Hur, Ina ta jiranka.” Hur ya fadi bisa kafafun Imam Hussain yana cewa “Ya shugabana, ka yafe mani don Allah, don Allah ka yafe mani, ina mai matukar nadamar abinda na aikata, ya kaicona.”
Imam Hussain ya kama kafadun Hur, yana ce masa “Hur, ya abokina na yafe maka, ina tabbatar maka cewar Kakana, Babana da Mahaifiyata sun yafe maka, taho gareni ya Hur.” Suka kama hanya zuwa sansanin Imam Hussain.
Hur yayi zabi mafi inganci, ya samu Imam Hussain mai yawan afuwa da gafara, Hur ya zabi zama ‘yantacce maimakon zinari da dirhamomi ko zama a cikin kaskanci da azaba mai tsanani gaban Allah Ta’ala gobe kiyama.
Bayan Imam Hussain ya jagoranci sahabbansa da iyalansa sallar azahar, sai maita da kwadayin fara yaki ya kara tsananta daga Yazidawa, suka ci gaba da kada kugen yaki da yunkurin kawo hari. Hur kuwa ya kasance cikin shauki da kwadayin kasancewa na farkon wanda zai fara shiga filin yaki yin mubaraza domin kare Hussaini dan Fatima al- Zahra (as). Don bada kariya ga addinin Allah, sai Hur ya fara neman izini daga Imam Hussain.
Imam Hussain yace masa “Ya Hur kai bako na ne, ka kasance tare dani na lokaci ne dan kalilan. Ban samu nayi maka hidima yarda ya kamata ba, ban iya na baka ko ruwa ba bare abinci. Kadan zauna tare dani mana koda dan kadan ne mana akalla. Ya Hur kai bako na ne , ba zan bari a kasheka ba.”
Hur, babu abin da zuciyarsa take hange sai daukakar da zai samu gobe kiyama idan har ya rabauta da samun shahada a wannan rana. Yana tunanin girman matsayin bada rai domin kariya ga dan Manzon Allah, musamman a irin wannan rana kuma a wannan wuri, don haka sai ya kasa hakura yaci gaba da rokon Imam Hussain akan bukatarsa. Imam Hussain ya fara tunanin idan Hur yaci gaba da zama tare da su, to zai fuskanci irin matsalar da ake fuskanta a sansanin ta fama da kishirwa da yunwa, don haka Imam Hussain ya amsa wa bukatar Hur, aka bashi izini, ya kama masa ya hau dokinsa.
Hur dama ya kasance jarumi ne, don haka Yazidawa basu ji dadi ba a hannunsa, don haka sai da suka yi masa taron dangi, suna sara da takubba, suna jifa da masu kuma suna harbi da kibau. Raunukan da suka ji masa yasa ya fado akan dokinsa jina-jina ya fadi kwance yana kiran Imam Hussain “ya shugabana! zo da sauri, ko na samu ganinka na karshe!”
Imam ya rugo ya dauke shi ya kwantar da shi a cinyarsa, yana masa bushara da cewa, Manzon Allah (S.A.W.A.) da Sayyida Fatima (A.S) suna jiran tarbansa. A wannan hali Hur ya tafi zuwa ga Ubangijinsa yana yardajje, ‘yan tacce wanda bai yarda da zama a cikin zilla ba. Imam Hussain da Abbas suka dauki gawarsa suka kai sansanin Imam Hussain. Inna Lillahi wa inna Ilaihi raji’un.